Labarai
Wani Maigadi Ya Sace ‘Ya’yan Ubangidansa a Minna
Daga Aliyu Lawal
Wani maigadi a garin Minna na Jihar Neja ya yi batan dabo da ’ya’yan ubangidansa su biyu.
Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Brighter da ke Minna a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da mahaifin yaran, wanda ɗan kasuwa ne, ya kasa gano inda ’ya’yansa Umar da Anas masu shekara shida-shida suke. Daga bisani ya fara zargin cewa Maigadin ne ya gudu da su.
Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Danjuma, mahaifin yaran, ba ya gida a ranar Lahadi da rana. A wannan lokacin ne maigadin gidan nasa mai suna Sani Abdulrahman, ya fita da yaran domin shagulgulan Sallah a kan babur da Alhaji Danjuma ya saya masa.
Rashin ganinsu na wani tsawon lokaci ne ya sa iyayen yaran suka fara bi asibitoci daban-daban a cikin birnin Minna, domin sun fara tunanin ko sun sami hatsari ne. Sai dai daga baya aka gano cewa yaran na hannun waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Da yake bayani kan lamarin, Alhaji Danjuma ya ce daga baya a wannan ranar wasu mutane sun kira shi daga dajin Erena da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, inda suka buƙaci ya kawo kuɗin fansa domin a sako ’ya’yansa da suke riƙe da su.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja da hukumomin tsaro da su taimaka wajen tabbatar da kuɓutar da yaran cikin koshin lafiya. Haka kuma ya roƙi al’umma da su taya su addu’are Allah Ya kubutar da yaran.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara ɗaukar matakan gaggawa domin gano inda yaran suke da kuma ceto su.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
