Labarai
Kano Na Fadada Ayyukan Kiwon Lafiya Domin Rage Mace-macen Mata Masu Juna Biyu
Daga Khadijah Aliyu
Gwamnatin Jihar Kano ta kara kaimi wajen aiwatar da shirin raba ayyukan jinya da musayar aiki wato (TSTS) a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, da na biyu domin inganta harkokin lafiya da rage mace-macen mata masu juna biyu, musamman a yankunan karkara.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano (SPHCMB), Salisu Shehu, ne ya bayyana hakan yayin wani taro kan daidaita shirin TSTS a bangaren Lafiyar Mata, Jarirai da Yara tare da Tsare-tsaren Iyali (MNCH/FP) wanda kungiyar KanSLAM ta shirya.
Farfesa Shehu ya bayyana cewa an kirkiro da wannan tsari da gwamnatin tarayya da jihohi suka amince da shi domin magance karancin kwararrun ma’aikatan lafiya a yankunan da ke da wahalar isa da kuma marasa wadataccen kulawa.
A cewarsa, shirin na bai wa ma’aikatan lafiya masu karamin matsayi damar gudanar da wasu ayyukan da a baya kwararrun likitoci ko jami’an lafiya masu manyan kwarewa kadai ke yi, karkashin kulawa ta musamman.
Ya ce shirin ya fara ne da inganta kula da mata masu juna biyu kafin haihuwa, gwajin fitsari da kuma ayyukan daukar hoton ciki (ultrasound) a cibiyoyin lafiya na matakin farko ta hanyar horas da ungozoma da ma’aikatan lafiya na al’umma.
“Sai dai karkashin shirin gwamnatin tarayya na rage mace-macen mata masu juna biyu mai suna MAMII, an fadada aikin zuwa ganowa da kula da yawan zubar jini, hawan jini mai haddasa jijjiga (eclampsia), karancin jini, cututtuka da zubar jini bayan haihuwa, da yayin daukar ciki da haihuwa.”
Farfesa Shehu ya ce yanzu ana horas da ma’aikatan lafiya da ke sahun gaba yadda za su auna yawan jinin da mace ta rasa yayin haihuwa ta amfani da kayan awo na musamman, gano alamomin boyayyiyar cuta, da kuma bayar da agajin gaggawa kafin tura mara lafiya zuwa asibiti.
Ya kara da cewa an kuma fadada shirin domin kula da cututtukan yara kamar zazzabin cizon sauro, da kuma ciwon rashin abinci mai gina jiki wato Tamowa, da cututtuka a matakin al’umma.
Haka kuma ya bayyana cewa Jihar Kano ta bullo da wani shirin jagoranci da sa ido, inda aka tura kwararrun likitoci da nas-nas zuwa kananan hukumomi domin duba aikin ma’aikatan lafiya da tabbatar da aiwatar da manufar yadda ya kamata.
Duk da nasarorin da aka samu, ya ce karancin wayar da kai, matsalolin sufuri da kuma jinkirin neman kulawar lafiya na daga cikin manyan kalubalen da ke shafar kula da lafiyar mata masu juna biyu a yankunan karkara.
A cewarsa, shirye-shiryen motocin daukar marasa lafiya na gaggawa da aka samar ta hannun NEMSAS, SEMSAS da RESMAT sun taimaka wajen daukar mata masu juna biyu daga kauyuka zuwa cibiyoyin lafiya, inda sama da mata 12,500 suka amfana da shirin cikin watanni kadan.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
