Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Wasu Sabbin Ka’idoji Kan Digirin Girmamawa
Daga Bello Wakili
Gwamnatin Tarayya ta amince da wani sabon tsari game da bayar da digirin girmamawa (honorary degrees) a jami’o’in Najeriya, a wani yunkurinta na kare martabar ilimi.
Ministan Ilimi, Farfesa Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayani a Abuja.
Ya ce sabon tsarin na da nufin kawo karshen bayar da irin wadannan digiri ba bisa ka’ida ba ko kuma ga wadanda ba su cancanta ba, tare da tabbatar da cewa ana ba da irin wannan girmamawa ne kadai ga mutanen da suka bayar da gudunmawa ta musamman wajen cigaban kasa, ilimi da kuma jin kai ga al’umma.
Ministan ya kara da cewa a karkashin sabbin ka’idojin, dole ne a bayyana a fili cewa digirin girmamawa ne, domin hana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, yayin da aka haramta ba da irin wadannan digiri na girmamawa ga masu rike da mukaman gwamnati a halin yanzu.
Ya kara da cewa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa za su rika sa ido kan yadda ake bin wadannan ka’idoji domin tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata a duk fadin jami’o’in kasar.
Haka kuma Ministan Ilimin ya sanar da amincewa da Asusun Kasa na Bincike da Kirkire-kirkire (National Research and Innovation Development Fund), wanda aka kirkira domin karfafa bincike, kirkire-kirkire da ci gaban fasaha a fadin kasar.
A cewarsa, asusun zai samar da tsari mai inganci ga bincike da cigaba, tare da bayar da tallafi ta hanyar gasa, ya kuma inganta amfani da sakamakon bincike a aikace, sannan ya tallafa wa sabbin masu hazaka, ya kuma samar da dakunan gwaje-gwaje na zamani, tare da karfafa hadin gwiwar bincike na kasa da kasa.
Ya kuma bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta umarci Babban Lauyan Tarayya da ya shirya kudirin dokar zartarwa domin aikawa Majalisar Dokoki ta Kasa, don tabbatar da kafa asusun bisa doka.
A cewarsa, ana sa ran wannan shiri zai samar da kimanin dala miliyan dari biyar a duk shekara domin tallafawa bincike mai muhimmanci da sakamakonsa kai tsaye, wanda ya dace da bukatun cigaban Najeriya, yana mai cewa wannan wani babban mataki ne na gina tattalin arziki da ya dogara da ilimi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
