Labarai
Rukuni na Farko na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasar Saudiyya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Rukuni na farko na Alhazan Jihar Kwara su 374 ya sauka ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Ɗaya daga cikin jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Mahmud Bube, tare da jami’an Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON su 3 ne suka jagoranci Alhazan da aka ɗauka ta jirgin MaxAir, inda suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Babatunde Idi-Agbon da ke Ilorin da misalin ƙarfe 3 na rana.
Da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin saman, Shugaban ukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji AbdulKadri Abdulsalam, ya shawarci Alhazan da su kasance masu bin doka da oda yayin zamansu a Saudiyya.
Alhaji Abdulsalam ya kuma yaba wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake ci gaba da bayarwa, wanda ya tabbatar da fara aikin cikin nasara.
A nasa jawabin, Amirul-Hajj kuma Etsu Tsaragi, Alhaji Aliyu Abdullahi Kpotwa, ya buƙaci Alhazan da su kasance masu ladabi, su kuma bi ƙa’idoji yadda ya kamata, tare da mai da hankali kan muhimmancin ibadar Hajji.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
