Labarai
Gwamnatin Nasarawa ta Nada Sabon Osu Ajiri na Masarautar Udege
Daga Aliyu Muraki
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta amince da nadin Suleiman Ahmed Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na masarautar Udege da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar.
Kwamishinan Kananan Hukumomi, Harkokin Masarautu da cigaban Al’umma na jihar, Alhaji Aminu Mu’azu Maifata ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.
Ya ce sabon basaraken zai fara aiki ne nan take, yana mai taya shi murna da kuma masa fatan alheri bisa nauyin da aka damka masa.
Alhaji Aminu Mu’azu Maifata ya kuma bayyana cewa an gudanar da nadin ne bayan tattaunawa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.
Ya ƙara da cewa Suleiman Ahmed Eko ya gaji marigayi Alhaji Halilu Bala-Usman tsohon mataimakin gwamnan tsohuwar Jihar Plateau, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayun 2025.
An haifi sabon basaraken ne ranar 2 ga watan Yunin 1972, ya kuma kammala karatunsa ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Nasarawa. Haka kuma yana da aure tare da ’ya’ya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
