Labarai
Harin Shanga: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafawa Iyalan Jama’an Tsaro da Aka Kashe
Daga Bello Wakili
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa iyalan jami’an tsaro da aka kashe a wani harin baya-bayan nan da ya faru a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi cewa za ta ci gaba da kula da walwalarsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan tabbaci a Birnin Kebbi yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamna Nasir Idris, biyo bayan kisan jami’an tsaro goma sha ɗaya da kuma rasuwar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, a birnin Alkahira na ƙasar Masar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya a madadin Shugaba Bola Tinubu, ya ce sadaukarwar jami’an da suka rasu ba za ta tafi a banza ba, yana mai jaddada cewa walwalar jami’an tsaro da iyalansu na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta sa a gaba.
Ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar da tallafin agaji ga iyalan da abin ya shafa da kuma al’ummomin da suka rasa matsugunansu.
Kashim Shettima ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu, tare da yin faran alkhairi ga al’ummar jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
