Labarai
Gidauniyar NASARA Ta Raba Kayayyakin Ramadan da na Sallah ga Marasa Galihu
Daga Sani Dutsinma
Marayu da zawarawa sama da dubu ɗaya ne suka amfana da tallafin kayayyakin Ramadana da na Sallah daga Gidauniyar NASARA a Jihar Kebbi.
Babbar Sakatariyar Yaɗa Labarai ta Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Khadijat Saidu ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce an bada tallafin ne domin sanya farin ciki a zukatan marayu da zawarawa 1,000 a garin Kangiwa, a watan Ramadan da kuma bukukuwan Sallah.
Ta ƙara da cewa, Gidauniyar NASARA wadda Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris ta kafa, ta raba kayan Sallah ga marayu, yayin da aka bai wa zawarawa buhunan shinkafa domin su sami damar yin bukin Sallah cikin farin ciki tare da iyalansu.

Tawagar gidauniyar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdulrasheed Bala, wanda shi ne jami’in da ke kula da Gidauniyar a matakin jiha, ta isar da saƙon Uwargidan Gwamnan, inda ta jaddada muhimmancin kyautatawa da nuna karamci, musamman a wannan lokaci na watan Ramadan.
A cewarsa, wannan kyakkyawan shiri na daga cikin ƙoƙarin Hajiya Zainab na tabbatar da cewa kowa yana cikin annashuwa a wannan lokaci na ibada. Ya ƙara da cewa ayyukan alherin da gidauniyar ke yi suna da matuƙar tasiri a rayuwar marasa galihu.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da gode wa Allah Madaukakin Sarki, sannan suka nuna matuƙar godiya ga wadda ta kafa gidauniyar, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, da kuma tawagar Gidauniyar NASARA bisa wannan karamci da kulawa da suka nuna.

-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
