Kasuwanci
Daliban BUK 300 Za Su Ci Gajiyar Horon Aikin Gona don Kasuwanci
Cibiyar Noma a Yankunan Busassu (Centre for Dryland Agriculture – CDA) ta Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta haɗa gwiwa da Ƙungiyar Ci Gaban Mata Manoma (Women Farmers Advancement Network – WOFAN) da kuma Kwalejin Aikin Gona, domin horas da daliban aikin gona 300 a duk shekara kan harkokin noma don kasuwanci da ƙara darajar amfanin gona, sarrafawa da kuma samarwa, ƙarƙashin shirin SIBLING Project.
Shirin, wanda ya shafi daliban matakai na aji 3 zuwa 4, an bayyana shi ne yayin wata ziyarar girmamawa da tawaga ta haɗin gwiwa daga WOFAN, CDA da Kwalejin Aikin Gona suka kai wa Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa.
A ƙarƙashin shirin, CDA ta ware filin gwaji mai girman hekta biyu, yayin da Kwalejin Aikin Gona ta samar da hekta 25 domin noman manyan gonaki da horo na aikace-aikace.
Shirin zai kuma bai wa dalibai damar fahimtar darajar noma da kasuwancin noma da kwarewar aikace-aikace da ke taimakawa bunƙasa aiki mai ɗorewa.
Da yake jawabi a lokacin ziyarar, Farfesa Haruna Musa ya yaba da haɗin gwiwar, inda ya bayyana ta a matsayin muhimmin tsari na ƙarfafa matasa da mata, yana mai nuna cewa mata 180 ne daga cikin daliban 300 da za su amfana da shirin.
Da yake karin haske kan haɗin gwiwar, Daraktan CDA, Farfesa Sanusi Gaya Mohammed, ya bayyana cewa CDA da WOFAN sun samu damar amfani da rumbun ajiya na ƙasa ta hannun Cibiyar Ƙasa ta Inganta Ayyukan Rumbunan Ajiya ta Nijeriya (National Storage Productivity Institute of Nigeria).
A nata jawabin, Daraktar WOFAN a ƙasa, Dakta Salamatu Garba, ta ce shirin na da nufin sauya yadda mata da matasa ke shiga harkar noma ta hanyar basu kwarewa, samun filayen noma da kayan aiki, tare da kasuwa mai tabbas.
Shi ma yana jawabi, Dekan Kwalejin Aikin Gona, Farfesa Muhammad Auwal Hussain, ya ce shirin ya samo asali ne daga buƙatun dalibai da matan ma’aikata, tare da haɗa al’ummomi biyu daga yankin Zango domin ƙarfafa hulɗar al’umma da ci gaba mai haɗa kowa da kowa.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
