Labarai
Gwamnatin Bauchi Za Ta Biya Kashi 50 Na Cikon Kudin Aikin Hajji
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da biyan kashi hamsin bisa dari na cikon kudaden aikin Hajjin 2024 ga Alhazan jihar.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi, na karin Nera Miliyan daya da dubu dari tara da goma sha takwas, kan Nera Miliyan hudu da dubu dari shida da suka biya a baya.
A don haka ne gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad ta kudiri aniyar bada tallafi ga Alhazan jihar, inda za a biya wa kowani maniyyaci Nera dubu dari tara da hamsin da tara.
Gwamnan ya amince da a biya Nera Miliyan dubu biyu da dari daya da casa’in da shidda domin tallafawa maniyyatan jihar su dubu biyu da dari biyu da casa’in.
Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
