Connect with us

Ilimi

Malaman Jami’ar Kwara Sun Yi Zanga-Zangar Lumana

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kwara da ke Malete (KWASU), ta gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Laraba domin neman a biya su kudaden alawus-alawus na EAA da  sauran hakkokinsu.

Malaman a karkashin inuwar ASUU sun ce sun shiga sahun sauran rassan kungiyar a fadin ƙasa wajen matsa lamba kan gwamnatin tarayya da ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da ASUU tun shekarar 2009.

Shugaban  ASUU reshen KWASU, ya bayyana cewa jinkirin biyan EAA da sauran hakkoki ya sanya malamai cikin mawuyacin hali, inda da yawa daga cikinsu ke fama da matsalolin tattalin arziki.

Ya ce duk da ƙalubalen da suke fuskanta, malamai na ci gaba da gudanar da ayyukansu na koyarwa da bincike, sai dai yanzu tura ta kai bango.

Mun fito ne domin nuna damuwarmu da kuma jawo hankalin gwamnati. Babu shakka, ci gaban ilimi ba zai yiwu ba idan malamai ba su samu kulawa da gata ba,” In ji shi.

Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Kwara da ya yi wajen ganin an warware matsalar cikin gaggawa.

ASUU ta yi gargadin cewa, idan aka ci gaba da watsi da bukatunsu, ba za su yi jinkiri ba wajen ɗaukar matakan da suka fi wannan tsauri a nan gaba.

Ta yi kira ga ɗalibai, iyaye da sauran jama’a da su fahimci matsayin da suke ciki, tare da goya musu baya wajen kare martabar ilimi da neman hakkinsu.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara