Labarai
KWEPA Ta Rufe Otel Takwas A Ilori
Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Kwara (KWEPA) ta rufe otel guda takwas a Ilori saboda kin bin ƙa’idojin da aka kafa na gudanar da harkokin otel a jihar.
Da yake magana kan lamarin a Ilorin, babban manajan hukumar, Jide Aina, ya bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan sanarwa da gargaɗi da dama da aka aika musu tun da farko.
Babban Manajan wanda shugaban sashen kula da otel, Malam Aminullahi AbdulRahman ya wakilta, ya ce an ba wa waɗannan otel ɗin isasshen lokaci don gyara ayyukansu, amma suka ci gaba da yin watsi da umarnin hukumar.
Ya jaddada cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa ga dokar muhalli ta jihar Kwara, inda ya ce ba a yi hakan da wata mummunar manufa ba, sai dai mataki ne da ya zama wajibi domin dakile karya doka da kuma kiyaye ƙa’idojin kiwon lafiya.
Jide Aina ya kuma bayyana cewa tilasta bin doka a sashen harkokin otel zai taimaka wajen kare rayuwar mazauna yankin, inganta lafiyar jama’a, da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu saka hannun jari da masu yawon buɗe ido.
Babban manajan ya sake tabbatar da jajircewar hukumar wajen yin haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin otel domin inganta ci gaban ɗorewa da kuma ɗaukar alhakin kare muhalli a jihar.
Ya kuma ja hankalin sauran masu harkokin otel da su bi ƙa’idojin muhalli da na gudanarwa gaba ɗaya don kauce wa irin wannan mataki.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
