Kasuwanci
Dikko Radda Ya Kafa Dokar Haramta Ɓoye Kayan Abinci A Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya sa hannu kan dokar da za ta haramta wa ’yan kasuwa da kamfanoni boye kayan abinci.
Gwamnan ya kuma kafa wani kwamiti na musamman da zai bi lungu da sako na jihar domin zakulo mutanen da ke boye kayan abinci a sassan jihar.
Har wa yau, an kayyade nau’ikan kayan abinci da dokar za ta yi aiki a kansu da suka hada shinkafa, masara, gero, dawa, waken suya, gyada da duk wani nau’in kayan abinci da karancinsa zai jefa Katsinawa cikin halin ha’ula’i.
Dokar ta fayyace karara cewa duk wani mutum ko kamfani da aka samu da laifin boye kayan masarufi, za a iya hukunta shi karkashin sashe na 114 a kundin manyan laifuka na final kod.
Haka kuma, duk wani wurin da aka kama ana boye nau’ikan kayan abincin da dokar ta kayyade, za a bude shi sannan a fitar da kayan abincin domin sayar wa al’umma a farashin da ya dace.
Kwamitin na kar-ta-kwana mai mambobi 27 da Gwamna Radda ya kafa ya umarci jami’an tsaro da su kamo tare da gurfanar da duk wadanda aka samu da laifin yi wa sabuwar dokar karan-tsaye.
kwamitin zai gana da masu ruwa da tsaki kan harkar kayan masarufi a jihar, inda zai rika kula da yadda ake safarar kayan abincin daga sassan jihar daban-daban da ma tsallakawa da shi da ake yi a kasashen waje.
Mambobin kwamitin sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Katsina, Alhaji Jabiru Salisu Abdullahi Tsari a matsayin jagora, sai Kwamishinoni a Ma’aikatar Shari’a da Yada Labarai da wakilan Sarakunan Katsina da Daura da wakilan kungiyoyin addini da ke jihar da sauransu.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
