Labarai
Sarkin Kano Na 16 Ya Yi Sabbin Nade-Nade A Kano
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya nada sabon Galadima na Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, tare da wasu manyan ‘yan Majalisar Sarki Masarautar su hudu.
Sabbin masu rike da mukaman gargajiya da aka yi wa rawani sun hada da Wamban Kano, Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Turakin Kano, Alhaji Mahmud Ado Bayero, Tafidan Kano, Adam Lamido Sanusi, da Yariman Kano, Alhaji Ahmad Abbas Sanusi.
Da yake jawabi bayan bikin nadin, Sarki Sanusi ya shawarci sabbin sarakunan da aka nada da su kasance masu koyi da shugabanni, inda ya ce sun riga sun nuna biyayya, tawali’u da tausayin talaka.
Ya bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma, ya kuma bukace su da su ci gaba da yin koyi da magabata.
Bikin kaddamarwar ya samu halartar gwamnan jihar Abba Yusuf da sauran ‘yan majalisar zartarwa na jihar da shugabannin gargajiya da na addini da ‘yan uwa da abokan arziki da dai sauransu.
A wani biki na daban da aka gudanar a fadar Karamar Hukumar Nassarawa, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya nada Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, inda ya bayyana irin tsarin shugabancin da ke gudana a masarautar.
Cover /Abdullahi Jalaluddeen/Kano
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai3 hours agoAKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
