Labarai
Trump Na Shan Suka Kan Wallafa Hotonsa Na AI Sanye Da Kayan Fafaroma
Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan fafaroma.
Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House.
Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen sabon fafaroma, bayan alhinin da suke ciki na rasuwar jagoran ɗarikar, Fafaroma Francis, wanda ya mutu ranar 21 ga watan Afrilu.
Taron mabiya ɗarikar Katorlika na birnin New York ya zargi Shugaba Trump da zolayar Addininsu.
Wallafa hoton na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya zolayi wani mai bayar da rahotonni da cewa ”ina son zama fafaroma”
Ba Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taɓa zarga da zolayar mabiya ɗariƙar Katolika ba.
A shekarar da ta gabata ma an zargi tsohon shugaban Amurka, Joe Biden lokacin da ya sanya hannu kan alamar kuros a lokacin wani gangamin masu goyon bayan zubar da cikin a Tampa da ke jihar Florida
A ranar Laraba mai zuwa ne fadar Vatican za ta fara shirye-shiryen zaɓen sabon fafaroma.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
