Labarai
Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki.
Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Birnin Kebbi.

Ya kuma yi alkawarin tabbatar da jin daɗin mahajjatan jihar yayin da suke a ƙasa mai tsarki.
Amirul Hajjin ya bayyana cewa jimillar mahajjata 3,800 daga jihar ne suka biya kuɗin kujerunsu gaba ɗaya domin aikin hajjin bana, kuma jigilar mahajjatan za ta fara ne ranar 9 ga watan Mayu, inda ya ce da yardar Allah za a ci gaba da jigilar ba tare wani tsaiko ba har sai an kammala.
Ya kuma bayyana cewa, a wannan shekarar, za a yi wa mahajjata canjin kuɗin guzirinsu na BTA zuwa kudin Saudiyya wato riyal kai tsaye, da nufin dakile ayyukan damfara da kuma kare mahajjata daga asarar kuɗi yayin musayar kuɗaɗe a nan gida da kuma Saudiyya.

Alhaji Muhammadu Mera ya shawarci mambobin tawagar gwamnati da jami’an hukumar jin daɗin mahajjata da su gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah, tare da kare haƙƙoƙin mahajjata, daidai da manufar Gwamna Nasir Idris na gudanar da sahihin aikin Hajji mafi kyau.
Shugaban Hukumar, Alhaji Faruk Musa Yaro, ya yi alkawarin bayar da cikakken haɗin kakaga tawagar gwamnati domin tabbatar da nasarar aikin Hajji da ba a taɓa irin sa ba a tarihin jihar.
Ya ce an riga an samu masauki da sauran abubuwan buƙata ciki har da sufuri da abinci a ƙasa mai tsarki, sannan kuma kamfanin jirgin samsada ya yi jigilar Alhazan jihar a shekarar da ta gabata, wato Flynas, a bana ma shi ne zau yi jigilar mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.
Haka kuma, an an fara yi wa Amirul Hajj da sauran mambobin tawagar gwamnati allurar rigakafi yayin kaddamar da shirin rigakafin mahajjatan.
Daga Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
