Kasuwanci
An Bada Umarnin Sake Tsugunar Da Wadanda Harin ‘Yan Bindiga Ya Rutsa Da Su A Kebbi
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa.
Gwamnan, ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kangiwa da Lakurawa suka kai musu hari tare da raba su da muhallansu a kauyukan Birnin Debe, Dan Marke da Tambo.
Gwamnan ya ce, ya kai ziyarar ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba shi damar samun rahoton halin da ake ciki a kan wannan mummunan lamari don jagorantar gwamnatin jihar ta dauki matakin da ake bukata tare da tantance halin da ake ciki da kuma tabbatar da matakan da suka dace da za a dauka cikin gaggawa domin kai daukin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
A yayin da yake koka da cewa, ana kai hare-haren ne daga jihar Sokoto da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi, ya kuma yaba wa jami’an tsaro da suka yi iya kokarinsu wajen ganin an shawo kan lamarin, ya kuma bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi da suka samu ga hukuma domin daukar matakin da ya dace.
Tun da farko Shugaban Karamar Hukumar Arewa Alhaji Sani Aliyu ya godewa Gwamnan bisa daukar matakin gaggawa don ganin an shawo kan wannan mummunan lamari.
Shugaban ya kuma bayyana cewa an bayar da agajin ga wadanda abin ya shafa, inda ya ce iyalan kowannen wadanda suka rasa rayukansu sun samu Naira 500,000 yayin da kowanne daga cikin wadanda suka jikkata kuma ya samu N500,000.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindigar Lakurawa suka kai hari kauyuka 7 a karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi inda suka kashe sama da mutane 10 tare da kona gidaje da dama wanda hakan ya kasance harin ramuwar gayya biyo bayan kashe wani shugabansu mai suna Maigemu da jami’an tsaro suka yi.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
