Connect with us

Ilimi

Mutane Dubu Biyar Suka Amfana Da Likitocin Sojoji

Published

on

 

 

Rundunar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto sun fara aikin ba da magani a wani bangare na bikin makwanni da tunawa da ‘yan mazan jiya da aka gudanar a karamar hukumar Dange Shuni.

 

A ci gaba da gudanar da bukukuwan tunawa da ranar tunawa da sojojin kasar na bana, a ranar Litinin din da ta gabata an bayar da aikin jinya kyauta ga mutane da ba su gaza 5,000 a Gidan Gabas, karamar hukumar Dange/Shuni ta jihar Sokoto.

 

Da yake jawabi, babban jami’in runduna ta 2 kuma kwamandan sashe na 2, Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Ibikunke Ajose, ya ce an gudanar da wannan shirin ne na wayar da kan jama’a na kiwon lafiya kyauta da nufin inganta huldar jama’a na rundunar soji domin inganta zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasa. .

 

Janar Ajose, wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta 8, Brig. Janar Ogbonnaya Igwe, ya ce “hakan kuma wani bangare ne na al’adar sojojin Najeriya da ta ta’allaka wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ga al’ummar da suka karbi bakuncinsu.

 

A nasa bangaren, Kwamandan Asibitin Kiwon Lafiya na rundunar, Brig. Janar Austin Okafor, ya ce aiki ya shafi masu cin gajiyar su dubu biyar da suka hada da gwaje-gwaje da kuma maganin zazzabin cizon sauro, hauhawar jini, maganin ido, samar da gilashin ido da kuma ayyukan hakora, tantance masu ciwon sukari da ayyukan kula da yara.

 

Brig. Janar Okafor ya bayyana cewa, duk wata babbar matsala da ba za a iya magance ta ba, za a kaita asibitin sojoji dake Barikin Giginya, Sokoto, domin samun kulawar da ta dace.

 

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Alhaji Abubakar Maradun, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya inda ya jaddada cewa daukar wannan mataki zai taimaka matuka wajen inganta lafiyar al’umma a yankin.

 

Abubakar ya roki sojojin da su kara kaimi ganin wannan tallafin ya isa ga sauran al’ummomi tare da ci gaba jihar.

 

Ya kuma roki jama’a da su yi wa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede da daukacin sojojin Nijeriya addu’a domin samun nasara da kuma gudanar da ayyukansu ga kasa.

 

NASIR MALALI/Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara