Kasuwanci
‘Yan Najeriya 390 da suka makale sun dawo gida daga Jamhuriyar Nijar
An dawo da wani sabon rukunin bakin haure ‘yan Najeriya 390 da suka makale a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar zuwa gida Najeriya.
Wadanda suka dawo sun isa makarantar horar da shige da fice ta Najeriya da ke Kano a ranar Talata da karfe 1:05 na safe.
Kungiyar ta kunshi manya maza 387, manyan mata biyu, da jariri daya.
Ofishin Jakadancin Najeriya a Yamai da Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ne suka taimaka wajen dawo da su.
Kwamishinan Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa (NCFRMI), Tijjani Ahmed, ya yi maraba da ‘yan gudun hijirar tare da jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na mayar da su ga iyalansu
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wannan shi ne karo na uku da suka dawo daga jamhuriyar Nijar, bayan wani yunkurin mayar da su gida a watan Disambar 2024, wanda ya dawo da ‘yan Najeriya 702 da suka makale.
Gwamnatin tarayya na kokarin tallafawa ‘yan Najeriya da ke makale a kasashen waje, inda aka dawo da jimillar mutane 5,219 daga kasashen Nijar, Libya da sauran kasashe tsakanin watan Fabrairu zuwa Disamba 2023.
Tawagar jami’ai daga hukumomi daban-daban da suka hada da NCFRMI, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM), Hukumar Yaki da Fataucin Jama’a (NAPTIP) da kuma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano ne suka tarbi wadanda suka dawo
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
