Connect with us

Kasuwanci

Masu Bincike Sun Isa Zamfara Don Binciken Harin Kuskure Da Aka Kai Yankin Maradun

Published

on

Wata babbar tawaga daga hedikwatar rundunar sojin sama ta Najeriya ta isa jihar Zamfara domin gudanar da tantancewar sakamakon harin da jirgin ya afku a jihar.

 

Tawagar ta samu jagorancin Air Vice Marshal (AVM) Edward Gabkwet, ta kuma kai ziyarar ban girma ga gwamna Dauda Lawal a gidan gwamnati tare da jajantawa gwamnatin jihar kan lamarin.

 

Air Vice Marshal Gabkwet wanda ya baiwa Gwamna Lawal tabbacin jajircewar rundunar wajen yaki da ‘yan fashi da kuma maido da zaman lafiya a jihar da ke fama da rikici, yana mai cewa, yaki da ta’addanci ya zama dole a yankin.

 

Ya kuma jaddada cewa, rundunar sojin saman Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukanta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

 

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa rundunar sojojin saman Najeriya bisa wannan ziyarar da suke yi da kuma kokarin da suke yi na tunkarar kalubalen tsaro da jihar Zamfara ke fuskanta.

 

Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa na bayar da tallafin da ya dace ga jami’an tsaro.

 

Ya yi kira da a kara hada kai a tsakanin masu ruwa da tsaki a yaki da rashin tsaro.

 

Tawagar ta kuma ziyarci hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma daga bisani kuma ta zarce zuwa unguwar Tungar Kara domin tantancewa a nan gaba.

 

Hare-haren da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai a makon jiya Asabar, ta afkawa ‘yan banga da mazauna unguwar Tungar Kara bisa kuskure, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane.

 

 

 

AMINU DALHATU/Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara