Kasuwanci
Farashin Kayan Abinci Ya Karye – FG
Gwamnatin Tarayya ta ce farashin abinci ya ragu saboda ruwan sama, da yawan girbi, da kuma ingantattun manufofin gwamnati.
Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin tarayya Abuja.
Lokacin noman 2024 ya yi nasara sosai, inda manoma a duk faɗin ƙasar suka sami yawan amfanin gona. Gwamnati na kokarin dorewar wannan ci gaba ta hanyar tallafawa noman alkama a yankunan tuddai kamar jihar Taraba da kuma samar da kayan aikin noma na zamani ga manoma.
A cewar ministan noma Abubakar Kyari, an sayo taraktoci da sauran kayan aiki sama da 2,000 kuma ana rabawa manoma. A ci gaba da tabbatar da hakan, gwamnatin ta kuma mai da hankali wajen habaka noman Tumatir a yankin Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma, inda ake sa ran girbi a watan Mayu.
A lokacin noman rani, ya ce an shirya shirin noma karin hekta 400,000 na gonaki tare da inganta samar da taki domin taimakawa manoma wajen bunkasa noman su.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati ta dukufa wajen tallafa wa manoma da albarkatun da suke bukata domin samar da abinci mai yawa da kuma rage tsadar rayuwa. Ya ce bangaren noma na Najeriya yana kara karfi kuma zai ci gaba da inganta a shekarar 2025.
Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa abokan hadin gwiwa na ci gaba da nuna kwarin gwiwa a fannin noma a Najeriya. Ya yi nuni da cewa, ba a taba ganin irin wannan matakin na amana da hadin gwiwa ba, wanda ke nuna kyakkyawan tasirin manufofin gwamnati da ci gaban da ake samu a fannin.
Tare da ingantattun hanyoyin noma, ingantattun kayan aiki, da haɓaka samar da kayayyaki, Nijeriya na ƙara samun ƙwararan matakan aikin noma, tana samun ƙarin tallafi da haɗin gwiwa daga ƙungiyoyin duniya. Ministan ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da bunkasa wannan fanni domin kara bunkasa fannin da kuma karfafa samar da abinci a kasar.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
