Connect with us

Ilimi

Majalisar Wakilai Na Bukatar Sanin Dalilin Da Ke Sa Jirgin Kasan Abuja Kaduna Ke Goce Hanya

Published

on

Majalisar Wakila zata gayyaci Ministan sufuri domin ya yima yan Najeriya bayanin abinda ya janyo jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja yake sauka daga kan laying dogo Wanda hakan Kan iya haifar da mummunan hadari ga rayuwar fasinjoji.

jirgin bukaci a gudanar da bincike kan musabbin abin da ke sa jirgin kasan Abuja- Kaduna ke karkacewa daga layin dogo wanda Kan iya haifar da mummunan hatsari ga rayuwar fasinja.

Hakan ya biyo bayan Kudurin gaggawa ne da Danmajalisa Mai wakilar mazabar Makarfi Kudan a Jihar Kaduna Alhaji Uamr Shehu Ajilo ya gabatar a zauren Majalisar da aka amince dashi.

Da yake gabatar da kudirin Alhaji Umar Shehu Ajilo ya koka ganin yadda Jirgin ke yawan turgudewa daga layin dogo inda hakan ka iya shafar sufirin jiragen kasa duk da irin gudunmawar da sashen ke bayarwa wajen tsaron lafiya da dukiliyar al’umma baki daya.

To amma yanda jirgin kasan Kaduna – Abuja yake yawan karkacewa daga hanyarsa na haifar da barzana ga rayuwar fasinjoji, lamarin ya Sanya bukatar mu hadakai domin daukar mataki.

Ya ce ganin yadda jirgin kasan yake jigilar fasinjoji da kaya da dama daga Kaduna zuwa Abuja, sannan yana bada gagarumar gudunmawa a fannin ci cigaban tattalin arziki da alummar Najeriya akwai bukatar majalisar ta sauki mataka gaggawa son gudun jefe al’umma cikin halin ni ‘yasu.

Alhaji Umar Ajilo, ya Kara da cewa abin takaici ne yadda jirgin kasan ke yawan sauka daga layin dogo, na baya bayan nan shi ne wanda ya faru a tashar jirgin kasa ta garin Asha da ke Babban birnin tarayya Abuja inda ya bar fasinjoji kara zube bayan Wanda ya faru a makonni biyu da suka gabata.

Ya cigaba da cewa wajibi ne Majalisar Wakilai ta gudanar da bincike domin gani dalilan da suka sa Jirgin kasan Kaduna-Abuja ne kadai yake fuskantar irin wannan Matsalar domin kare aukuwar lamarin anan gaba.

Da take amincewar da kudurin Majalisar ta umarci kwamitinta ya gayyaci ministan sufiri da sauran Jagororin a bangaren sufurin jiragen kasan da su zo su yi mata bayani don lalubo hanyoyin maganve sake faruwar hakan a nan gaba.

Ana sa ran Kwamitin ya gudanar da binciken sa cikin makonni hudu da gabatar da rahoton sa a zauren majalisar don daukan Madaki na gaba.

COV : TSIBIRI

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara