Labarai
Senegal Ta Kama Tan Guda Na Hodar Ibilis
Hukumar Kwastam ta Senegal ta ce ta kwato fiye da tan guda na hodar ibilis a kudu maso gabashin kasar, inda ta bayyana shi a matsayin kamu mafi girma da aka taba yi na jigilar hodar iblis a kan hanyar kasa a yammacin Afirka.
Hukumar ce an kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram dubu daya da dari daya da talatin da bakwai da digo shidda a ranar Lahadin da ta gabata a garin Kidira, wacce ta kiyasta kudinsa zai kai sama da CFA biliyan 90, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 146.
Sanarwar ta ce, wannan shi ne kamu mafi girma na hodar iblis ta hanyar kasa da aka taba samu a Senegal.
Hukumar ta ce an boye hodar ne a cikin fakiti-fakiti kuma an sanya shi a cikin jakunkuna a wata mota mai daukar kayan sanyi da ta fito daga wata kasa mai makwabtaka da Senegal, wadda ba ta bayyana sunan kasar ba.
Kasar Senegal dai tana iyaka da kasashen Guinea da Gambia da Guinea Bissau da Mauritania da kuma Mali, kasashen da aka san su ne wuraren safarar magungunan da ake samarwa a Amurka ta Kudu akan hanyarsu ta zuwa Turai.
Yammaci da tsakiyar Afirka ya zama yankin da ake yawan amfani da shi, a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka.
A watan Oktoban 2022, an kama kilogiram 300 na hodar iblis daga wata motar daukar kaya masu sanyi da ta taho daga Mali.
Haka kuma Rundunar sojin Senegal a watan Nuwamban bara, ta ce ta gano kusan tan uku na hodar iblis daga wani jirgin ruwa a gabar teku.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
