Fasaha
Kotu ta tursasa a sauya sunan zakunan da aka yi wa laƙabi da abin bautar Hindu

Kotu a ke Indiya ta umarci wani gidan yari da ke jihar West Bengal ya canza wa wasu zakuna suna bayan wata ƙungiyar mabiya addinin Hindu ta yi koken cewa hakan saɓo ne ga addininsu.
Zakanya ta farko, tun asali an laƙaba mata suna wanda ya samo asali daga abar bautar mabiya addinin Hindu da ake kira Sita, sai kuma zakin da ake kira Akbar wanda shi ma ya samo asali daga wani jagora na daular Mughal a ƙarni na 16.
Ƙungiyar mabiya Hindu ta Vishwa Hindu Parishad ce ta ƙalubalanci hakan a kotu, kan cewa sunan da aka bai wa zakanyar saɓo ne a addinin Hindu.
A ranar Alhamis, kotun ta ce a daina sanya wa dabbobi sunayen abin bautar Hindu ko na annabawan Musulunci ko manyan malaman Kiristoci da na mutanen da suka lashe kyautukan Nobel da kuma na ƴan rajin ƙwatar ƴanci.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
