Ilimi
Jakadan Amurka Ya Ziyarci Sarkin Zazzau Domin Karfafa Alakar Amurka Da Najeriya
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu.
Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.”
A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen zurfafa wannan alaka ita ce ta haduwa irin wannan da za mu ji ta bakin juna.
“Ina sa ran jin ta bakinku kan abubuwan da kuke yi na karfafa hadin kan addini a tsakanin al’umma, damar ilimi da kuma damar yin aiki ga jama’ar ku.
“Abin da Amurka za ta iya yi don haɓaka ƙarin alaƙa da kuma matakan da za mu iya ɗauka don zurfafa dangantakarmu,” in ji Mills.
Da yake mayar da jawabi, Mai martaba Sarkin Zazzau ya yabawa ma’aikatar harkokin wajen Amurka kan bude cibiyar kula da harkokin a Amurka a jami’ar Ahmadu Bello.
Bamalli ya yi fatan wannan cibiar da aka kira da Window on America da turanci ta zama matakin samar da ingantacciyar dama tsakanin Amurka da masarautar Zazzau da jihar Kaduna.
Ya kara da cewa masarautar na da alaka mai tsawo da ofishin jakadancin Amurka inda ya kara da cewa tawagogin ofishin jakadanci sun kasance suna halartar Dabar karshen watan Ramadan a Zariya.
“Amma hakan ya tsaya cik tsawon wasu shekaru saboda rashin tsaro, amma za mu iya cewa zaman lafiya ya dawo ga al’ummarmu.
“Saboda haka, muna fatan mambobin ofishin jakadancin da sauran jami’an diflomasiyya za su ci gaba da halartar bukukuwan Sallah Durbar,” in ji Bamalli.
COV/ Ibrahim Suleiman
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
