Connect with us

Labarai

An Kashe Jagoran Harin NDA Da Sace Daliban Birnin Yauri

Published

on

Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Boderi, wanda ya kitsa harin da aka kai makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna.

Boderi ne kuma ya kitsa hari da kuma sace dalibai a Jami’ar Greenfield da ke jihar, da kuma ’yan matan makarantar sakandaren Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya sanar.

Sanarwar ta ce cewa a ranar Laraba aka kashe Boderi ne tare da wani shugaban ’yan bindiga mai suna Bodejo a kan hanyar Bada–Riyawa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

“Majiyoyin leken asiri sun ba da rahoton cewa an kashe kasurgumin dan bindiga Boderi wanda ya kitsa sace daliban Birnin Yauri, Jami’ar Greenfield da kuma NDA, tare da wani mai suna Bodejo.

“Ana ci gaba da kokarin tabbatar da hakan ta hanyar amfani da wasu hanyoyi,” in ji sanarwar.

A cewarsa, kun kwato babura 19 da ’yan ta’addan suka gudu suka bari da wasu abubuwa, kuma an kona su.

a wani samame na daban da sojoji suka kai a yankin, “’yan ta’addan da suka yi amfani da shanu a matsayin garkuwa, sun bude musu wuta, amma suka mayar da martani cikin gaggawa.

“A yayin musayar wutar ta kusan awa daya, sojoji sun kashe biyu daga cikin ’yan ta’addan tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda 1, da sauran abubuwa.

“Sai dai kuma an kashe wasu daga cikin dabbobin satan da da ’yan ta’addan ke amfani da su a matsayin garkuwa.

“Sojoji na ci gaba da bin diddigin ’yan ta’addan da suka tsere da kuma aikinsu na samar da tsaro a yankin.”

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara