Labarai
‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Satar Limamai 6 A Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu limamai shida a kan hanyar Dakko zuwa Damri, a Ƙaramar Hukumar Bakura ta jihar.
An sace limaman ne ranar Asabar, 12 ga watan Satumban 2026, lokacin da suke tafiya zuwa Talata Mafara.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 da rabi na safe, lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi wa motar da limaman ke ciki kwanton bauna.
Ya ce bayan samun rahoton, jami’in ’yan sandan da ke kula da sashen Bakura ya tattara jami’an tsaro, ciki har da jami’an Sashen Yaki da Miyagun Laifuka, VCRU, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro gudanar da bincike a dazuzzukan da ke kewaye da wuraren da ake zargin ’yan bindigar sun nufa, domin kuɓutar da limaman da kama waɗanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya umarci jami’an da ke aikin ceto da su ƙara ƙaimi tare da amfani da dukkan dabarun da suke da su domin kuɓutar da waɗanda aka sace.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da sahihan bayanai cikin gaggawa, waɗanda za su taimaka wajen gano inda limaman suke, domin kuɓutar da su da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
