Labarai
Hajj2026: Mahajjata Sun Fara Tururuwa a Kasuwannin Makka
Daga Usman Muhammad Zaria
Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya da ake sa ran za su fara gudanar da ibadun aikin Hajji nan da ranar 25 ga watan Mayu, sun mamaye shaguna da manyan kasuwanni domin sayen tsaraba ga ‘yan uwansu da abokan arziki.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria daga Makkah ya ruwaito cewa, ya zama al’ada ga mafi yawan mahajjata su sayi tsaraba yayin aikin Hajji, saboda ana ganin duk wata kyauta daga ƙasa mai tsarki tana da muhimmanci da kuma armashi na musamman.
Mahajjatan na sayen tsarabe-tsarabe iri-iri da suka haɗa da tufafi, takalma, jakunkuna, turare, dabino, kayan wasa, darduma, kayan ado da kuma kayayyakin amfanin gida da sauransu.
Wasu daga cikin mahajjatan, Alhaji Abdullahi Ibrahim da Alhaji Salisu Ismail daga Malam Madori, sun ce kasancewar wannan ne Hajjinsu na farko, dukkan ‘yan uwansu na sa ran samun tsaraba daga gare su.
Sun ce, Kyaututtukan za su bambanta gwargwadon kusancinsu da, “ba za a rasa abin da za a bada tsaraba ga masoya ba komin kankantarta“. In ji su.
Sun kuma bayyana cewa daga cikin Dala 500 da aka ba su a matsayin kuɗin tafiya, sun tanadi ƙarin kudade tun kafin zuwansu ƙasa mai tsarki domin sayayya ta kansu da kuma tsaraba.
Wani mahajjaci, Alhaji Mubarak Musa Adamu daga ƙaramar hukumar Dutse, ya ce sayen tsaraba ga masoya da ‘yan uwa abu ne mai matuƙar muhimmanci, ko da kuwa ba Hajjin farko ba ne.
Ya ce, “Mutane suna daraja tsarabar da aka kawo daga Saudiyya, ko da dabino ne ko darduma ka saya musu, suna matuƙar jin daɗi saboda muhimmancin da ake danganta ta da ƙasa mai tsarki.”
Mahajjatan na yawan zuwa manyan kasuwanni da shaguna, yayin da wasu suke sayayya a bakin tituna.
Wasu daga cikin mahajjatan sun ce suna samun gamsuwa da kwanciyar hankali idan suna sayayya a manyan kasuwanni duk da tsadar kayayyaki, inda suka ce tsananin zafi da cunkoson jama’a na sanya yin sayayya a bakin hanya ya zama da wahala.
Sun ce, “Farashin kayayyaki a manyan otal-otal da kasuwanni yana da tsada, ‘amma ba mu damu ba saboda muna samun gamsuwa kuma shagunan suna da na’urar sanyaya wuri.”
An kammala dukkan shirye-shirye domin fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 wanda zai gudana na tsawon kwanaki huɗu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
