Connect with us

Labarai

Kauru: APC Ta Karfafa Hadin Kai Tare da Tabbatar da Goyon Bayan Tinubu da Uba Sani

Published

on

Daga Yusuf Zubairu Kauru

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna sun sake jaddada goyon bayansu ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani gabanin zaben shekarar 2027.

Masu ruwa da tsakin, tare da hadin gwiwar shugabannin jam’iyya a yankin, sun ce sabon hadin gwiwar da aka kulla na da nufin karfafa tattara magoya baya tun daga matakin karkara, da kuma tabbatar da nasarar APC a zaben.

Sun kuma goyi bayan tsarin rabon mukaman siyasa bisa a yankuna uku na Karamar Hukumar Kauru, wato Masarautar Kumana, Masarautar Chawai da Masarautar Kauru. Inda suka jaddada muhimmancin adalci, gaskiya da daidaiton wakilci.

A cewarsu, wannan tsarin rabon mukamai an tsara shi ne domin tabbatar da hada kai da kuma karfafa zumunci tsakanin al’ummomin da ke karamar hukumar.

Sanarwar da Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Bashir Tanko Dawaki ya fitar ta hannun Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Jama’a, Yahaya Sa’ad (Danruwatan Kauru), ta bayyana cewa masu ruwa da tsakin na da cikakken goyon baya ga gwamnatin Gwamna Uba Sani tare da kudurin inganta shugabanci nagari a fadin jihar.

Har ila yau, masu ruwa da tsakin sun bukaci a kara bai wa mata da matasa dama a harkokin jagoranci da yanke shawara. Sun ce wannan kokari ya yi daidai da salon shugabancin Gwamna Uba Sani na bai wa kowa dama da tabbatar da adalci.

Taron ya samu halartar masu neman takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna daga Masarautar Chawai, da kuma mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai daga Masarautar Kauru.

Mahalarta taron sun bayyana wannan zama a matsayin alamar hadin kai da kuma jajircewa wajen ganin APC ta samu nasara a zaben 2027. Sun sake jaddada kudurinsu na goyon bayan gwamnatin Gwamna Uba Sani da kuma inganta shugabanci nagari a jihar.

Masu ruwa da tsakin sun nuna kwarin gwiwa cewa hadin kai tsakanin Masarautar Kumana, Masarautar Chawai da Masarautar Kauru zai tabbatar da nasarar ‘yan takarar APC a zaben mai zuwa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara