Connect with us

Labarai

Ƙungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka Ta Bai Wa ‘Yan Sanda Injin Hilux Don Ƙarfafa Tsaro

Published

on

Ƙungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka SAPPEF a ƙaramar hukumar Lere ta Jihar Kaduna ta bayar da gudummawar sabon injin motar Hilux ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, reshen Saminaka, domin ƙarfafa tsaro da kuma inganta zaman lafiya a yankin.

Wannan kyauta na da nufin tallafa wa ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, musamman a cikin Masarautar Saminaka.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Shugaban kungiyar, Ma’ajin na SAPPEF, Alhaji Adamu Nuhu, ya bayyana cewa wannan gudummawa na daga cikin jajircewar ƙungiyar wajen inganta tsaron al’umma da kuma tallafa wa hukumomin tsaro.

Ya ƙara da cewa tsaro shi ne babban abin da kungiyar ke ba fifiko, kuma za su ci gaba da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Da yake jawabi yayin bikin miƙa gudummawar, mai martaba Sarkin Saminaka, Musa Mohammed Sani, ya nuna godiya ga kungiyar bisa wannan kyakkyawan mataki.

Ya bayyana cewa wannan gudummawa ta zo a kan lokaci, yana mai cewa gyarawa da inganta motar Hilux ɗin zai taimaka wajen inganta ayyukan tsaro da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma.

Sarkin ya kuma buƙaci sauran ƙungiyoyi da daidaikun mutane da su yi koyi da wannan mataki na tallafa wa hukumomin tsaro.

Haka kuma, Limamin Babban Masallacin Mangorori na Saminaka, Malam Shuaibu Yahaya, ya yi addu’o’in samun ci gaba da zaman lafiya, haɗin kai, da kuma shiriya daga Allah ga duk masu ruwa da tsaki.

Yusuf Zubairu/Sani Y

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara