Labarai
Gwamnan Zamfara Ya Bukaci Karin Hadin Gwiwar Sojoji Domin Magance Matsalar Tsaro
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen bai wa sojoji goyon baya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance matsalolin tsaro a jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, a wata ziyarar girmamawa da ya kai masa a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
Gwamna Lawal ya bayyana ziyarar ta Babban Hafsan Tsaron a matsayin wadda ta zo a kan lokaci, tare da nuna irin jajircewar rundunar sojojin ƙasar wajen magance matsalolin tsaron da ke addabar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
Ya ce kasancewar manyan hafsoshin soji a jihar zai zama babban gargadi ga masu aikata laifuka da ke kai hare-hare a jihar da kewaye.

Gwamnan ya jaddada cewa inganta tsaro a matakin al’umma na da matuƙar muhimmanci, yana mai cewa dawo da zaman lafiya a Zamfara zai taimaka matuƙa wajen rage matsalolin tsaro a faɗin yankin.
Dauda Lawal ya tuna da wani lamari da ya faru kwanan nan lokacin da mazauna ƙauyen Wanzamai suka tare ayarinsa domin nuna damuwarsu kan ci gaba da hare-haren ‘yan bindiga bayan janye jami’an tsaro daga yankin.
A cewarsa, koken da mata da yara suka yi ya nuna matuƙar buƙatar sake tura jami’an soji da samar da kariya a yankunan da ke cikin haɗari.
Ya ƙara da cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka ba su fi ƙarfin jami’an tsaron Nijeriya ba, amma ya jaddada buƙatar ingantaccen tsari da wadatattun kayan aiki, da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji domin murƙushe su.
Gwamnan ya kuma yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro duk da ƙalubalen da suke fuskanta, tare da alƙawarin ci gaba da bayar da goyon bayan gwamnatin jihar domin tallafawa ƙoƙarin gwamnatin tarayya.
Ya roƙi Babban Hafsan Tsaron da ya ƙara bai wa kwamandojin rundunonin da ke aiki a filin daga tallafi, ciki har da kwamandojin Theatre da Brigade, domin ƙara inganta ayyukansu.
Haka kuma ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar soji, tare da kira da a ƙara ƙarfafa matakan tsaro a matakin ƙasa da ƙasa.
Tun da farko, Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, ya ce ziyarar tasa na daga cikin ƙoƙarin duba yadda ayyukan rundunar Operation Fansan Yamma ke gudana da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin inganta tsaro a yankin.
Ya bayyana cewa ya duba ayyukan da ake gudanarwa a filin daga, inda ya ce an riga an magance wasu daga cikin matsalolin da sojoji suka fuskanta, yayin da ake ci gaba da nazarin wasu domin ɗaukar mataki.

Daga ƙarshe, ya nuna kwarin gwiwa cewa idan aka ci gaba da wannan haɗin gwiwa tsakanin sojoji, gwamnati da al’umma, za a samu nasarar rage ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifuka a Zamfara da ma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
Cov/Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
