Labarai
‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Bindiga Da Ceto Wasu Da Aka Sace A Zamfara
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta ce ta samu nasarori a ƙoƙarinta na yaƙi da ta’addanci, inda ta ceto wasu da aka sace tare da cafke wasu da ake zargi da aikata laifuka.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce da misalin ƙarfe biyu na dare ‘yan bindiga sun kai hari gidan wani ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya dake Kaura Namoda, Mamuda Buhari, inda suka sace shi tare da ‘ya’yansa uku.
Sai dai bayan samun rahoton lamarin, jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai suka bi sawun maharan, lamarin da ya kai ga ceto yaran uku, waɗanda aka mayar da su ga iyalansu.
Sanarwar ta ce ana ci gaba da kokarin ceto mutumin da har yanzu yake hannun maharan.
A wani lamari na daban kuma, ‘yan sanda sun cafke mutane biyu da ake zargi da zama ‘yan bindiga bayan sun kai hari ga jami’an tsaro a yankin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da farautar waɗanda suka tsere tare da rusa kungiyoyin masu aikata laifi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa yaƙi da ta’addanci.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
