Labarai
Tinubu: Sabbin Dokokin Haraji Za Su Kawo Wadata Yayinda Tsofaffi Suka Talauta ‘Yan Najeriya
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce tsofaffin dokokin haraji na zamanin mulkin mallaka sun talauta ‘yan Najeriya, yana mai cewa sabbin gyare-gyaren da gwamnatinsa ta kawo za su samar da dama da wadata ga al’umma.
Ya bayyana haka ne a Abuja yayin kaddamar da sabon hedikwatar Hukumar Haraji ta ƙasa, inda ya jaddada cewa tsarin harajin da aka ƙirƙira yanzu ya fi karkata ga jama’a da kuma jawo zuba jari.
Shugaban ya ce sabbin dokokin, da aka fara aiwatar da su a watan Janairu, za su gyara matsalolin tsohon tsarin tare da sanya tattalin arzikin ƙasar ya zama mai gasa a duniya.

A wajen taron, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas sun yabawa gyare-gyaren, suna cewa sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Shugaban ya kuma buƙaci hukumar haraji ta kasance mai gaskiya da inganci wajen aikinta, tare da gina amincewar jama’a, yana mai cewa hakan ne zai tabbatar da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Bello Wakili Abuja
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
