Labarai
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Taya Musulmi Murnar Sallah
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Dakta Danladi Jatau, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin Eid-el-Fitr na bana, tare da taya su murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Haka kuma, ya buƙaci Musulmi da su ƙara yawan addu’o’i domin samun dorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa da jihar, tare da fatan nasarar shugabanni a dukkan matakai.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Kakakin Majalisar, Jibrin Gwamna ya fitar, an rawaito Dakta Danladi Jatau na kira ga Musulmi da sauran al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, da sauran shugabanni addu’ar samun nasara a ayyukan da ke gabansu.
Kakakin Majalisar ya jaddada muhimmancin wannan biki da ya biyo bayan azumin watan Ramadan, inda ya buƙaci a yi amfani da wannan lokaci wajen yin nazari cikin natsuwa, tare da nuna ƙauna, fahimtar juna, sadaukarwa da kuma tausayi domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar ƙasa.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar muminai da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara kusanci da Allah da kuma kyautata hulɗa da ‘yan uwansu, musamman masu hali su taimaka wa marasa galihu domin su ji su ma suna cikin al’umma.
A ƙarshe, Dakta Danladi Jatau ya jaddada muhimmancin bin doka da oda da kuma biyayya ga hukumomi, tare da yi wa dukkan Musulmi fatan gudanar da bikin Sallah cikin nasara.
Aliyu Muraki/Lafia
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
