Labarai
Ƙungiyar NUJ–FRCN Kaduna Ta Kaddamar da Tallafin Ramadan ga Mambobinta
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen gidan rediyon tarayyar Kaduna, ta raba buhunan shinkafa da sukari ga mambobinta a matsayin tallafin domin saukaka musu a lokacin azumin Ramadan.
Shugaban kungiyar Umar Adamu Sarkinfada ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar gidan Rediyon Najeriya Kaduna da ke Kaduna.
Ya ce an dauki matakin ne domin rage wahalhalun da tsadar kayan abinci ke haifarwa, musamman a lokacin watan Ramadan da kudaden kayayyakin masarufi ke karuwa.
A cewarsa, duk da cewa kayayyakin ba za su cika bukatun membobin ba, an yi su ne don samar da dan agaji da kuma zama wata alama ta nuna godiya ga goyon baya da hadin kai da shugabancin ya samu.

Shugaban ya kuma yi bukaci mambobin kungiyar da su ci gaba da ba su goyon, ya kuma yi kira ga Musulmi da Kirista da su yi amfani da lokutan Ramadan da na Azumi wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da wadata.
Wasu da suka ci gajiyar shirin sun yabawa kwamitin zartarwar kungiyar bisa wannan shiri tare da karfafa gwiwar shugabanni da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na walwala tare da inganta hadin kai a tsakanin mambobin kungiyar.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
