Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Sama da Naira Biliyan 2 Don Hidimar Aikin Hajjin Bana
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar sama da Naira Biliyan 2 da miliyan 600 domin gudanar da ayyukan Hajjin 2026.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, amincewar da majalisar ta yi na da nufin tabbatar da sauƙaƙe jigilar maniyyata tare da kula da walwalarsu yayin tafiyar su zuwa kasar Saudiyya.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da kudaden ne wajen muhimman bangarorin ayyukan Hajji.
Alhaji Sagir ya ce hakan ya haɗa da sufurin jiragen sama, masauki, abinci, hidimomin lafiya, shirye-shiryen wayar da kai, da sauran shirye-shiryen dabaru da za su tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara ba tare da wata tangarda ba ga dukkan maniyyatan jihar.
Ya bayyana cewa, majalisar ta jaddada ƙudurinta na tallafa wa ayyukan ibada tare da tabbatar da cewa maniyyatan jihar sun gudanar da Hajjin su cikin mutunci, tsaro, da nagartaccen tsari, bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da kuma jagororin da hukumomin Hajji suka tanada.
Kwamishinan ya ce, majalisar ta tabbatar wa maniyyata da kuma al’umma gaba ɗaya cewa za a gudanar da dukkan shirye-shiryen Hajjin 2026 bisa gaskiya, da inganci.
Ya ƙara da cewa, hukumomin da abin ya shafa za su yi aiki tare domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2026 da kuma walwalar maniyyatan jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
