Labarai
Tsadar Kayan Aiki, Faduwar Farashi Na Barazana Ga Manoman Najeriya – Mikati
Daga Yusuf Zubairu
Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Masu Samar da Amfanin Gona ta Arewa maso Yamma NOWACAS, Shuaibu Idris Mikati, ya yi gargadin cewa manoman Najeriya na cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar noma, yayin da farashin amfanin gona ke kara faduwa.
Mikati ya bayyana wannan gargadin ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce halin da ake ciki abin damuwa ne ƙwarai domin zai iya haifar da karancin abinci a kasa muddin ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ya ce duk da cewa ana ganin kamar farashin abinci na da tsada idan aka kwatanta da naira, cikakken bincike kan musayar kuɗaɗe na ƙasashen waje yana nuna wani yanayi daban.
A cewarsa, idan aka auna farashin wasu amfanin gona da dalar Amurka, za a ga cewa a zahiri sun fi araha a yau fiye da yadda suke a shekarun baya.
Shuaibu Mikati ya ce a halin yanzu ana sayan buhun masara naira dubu 30, bayan da manoman da suka sayi taki kusan Naira dubu 100 kowanne buhu, wanda hakan ba karamar asara ba ce, kuma ba zai haifar da ‘Da dai ido ba.
Ya bayyana cewa a da, manomi na iya musanya buhun amfanin gona guda ɗaya da buhun taki ɗaya, amma a yau dole ne ya sayar da buhu biyu da rabi zuwa uku kafin ya samu buhun taki guda.

Ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar wa manoma kayan aiki da taki cikin sauƙi da rahusa ba, samar da abinci zai ragu ƙwarai, lamarin da zai zama babbar barazana ga wadatar abinci a Najeriya.
Shugaban NOWACAS ya soki manufofin gwamnati da ke ba da damar shigo da amfanin gona daga waje a farashin da ke gogayya da na gida ba tare da samar da ƙayyadadden farashin da zai zamto kariya ga manoman cikin gida ba.
A cewarsa, shigo da kayayyaki daga waje na rage darajar farashin amfanin gona na gida, yayin da manoman Najeriya ba su da wata kariya ko diyar da suke samu sakamakon asarar amfanin gona.
Mikati ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gaggauta zartar da dokar National Trust Receipt (Warehouse Receipt) da ta daɗe ana jira, wadda za ta ba manoma damar samun rance ta hanyar amfani da takardun rumbunan ajiya a matsayin jingina.

Ya kuma soki dakatar da tallafin kuɗaɗen noma sakamakon yadda wasu suka karkatar da kudaden a baya, yana mai cewa hakan ba adalci ba ne ga manoman gaskiya.
Mikati ya buƙaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya rika bada tallafin kuɗaɗen noma ta hannun Bankin Manoma na Kasa (Nigerian Agricultural and Cooperative Development Bank) domin tabbatar da ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Ya jaddada shirye-shiryen NOWACAS na yin aiki da gwamnati a kowane mataki, tare da yin kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙara kaimi wajen yada al’amuran da suka shafi manoma, yana mai cewa wadata kasa da abinci muhimmin ginshiƙi ne ga rayuwa da daidaiton tattalin arzikin Najeriya.
Yusuf Zubairu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
