Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Ilmantar da Fulani Maniyyata Gabanin Aikin Hajji

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudirinta na ci gaba da ilimantarwa tare da wayar da kan Fulani maniyyata kan yadda ake gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki.

Shugaban  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da Shugabannin Kungiyar Fulani suka ziyarce shi a ofishinsa dake Dutse babban birnin jihar.

Alhaji Ahmed Umar Labbo, yana mai cewar ilimantarwa tare da wayar da kan maniyyatan jihar musamman Fulani ya zamo wajibi, domin hukumar tana da malaman bita da za su taimaka masu wajen sauke farali tun daga nan gida Najeriya a da kuma kasar Saudi Arabia.

Ya kuma bada tabbacin yin aiki tare da kungiyar domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Labbo, yayi nuni da cewar, ililimi gudanar da aikin Hajji na da matukar muhimmacin gaske musamman ga mamaniyya Fulani, wanda hakan ya sa hukumar ke gudanar da bitar aikin hajji a aikace.

Ahmed Labbo yace gabatar da bita da yaren fillacin zai taimaka masu matuka su fahimci yadda za su gudanar da ibadar aikin hajji ingattacciya.

Tun farko a jawabin shi, Shugaban kungiyar Malam Mustapha Sa’idu Zakari yace manufar kungiyar itace ilimantar da fulani maniyata aikin hajji da yaren fulatanci domin su samu aikin hajji karbabbe.

Yace kungiyar tana da wakilai a dukkanin kananan hukumomin jihar 27 domin shiga rugagen fulani don koyar da su ilimin addini ta yadda zasu gudanar da aikin hajji ga wadanda Allah ya baiwa iko.

Malam Mustapha Zakari, ya kuma godewa hukumar jin dadin Alhazan bisa jagorancin Alhaji Ahmed Umar Labbo kan manufar sa wajen ilimantarwa tare da wayar da kan Alhazan jihar.

Labarai

Ilimi2 days ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai2 days ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha3 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai3 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai3 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai3 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci3 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara