Labarai
Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Zamfara dake Tsafe za ta bullo da sabbin tsare-tsare don inganta ayyuka.
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara (ZMSCHST) Tsafe ta bayyana shirin bullo da manufofin karfafa tsarin kwalejojin CSSP don inganta ayyukan kwalejin zuwa tsarin fasahar zamani.
Mukaddashin Shugaban Kwalejin, Malam Jamilu Lawal ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da shugabanin gudanarwa da daraktoci da shugabannin sassan da aka gudanar a Tsafe.
A cewar Malam Lawal, hukumar za ta yi nazari kan manufofin da ake da su tare da tsara wata sabuwar hanya ta ci gaban hukumomi.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na kwalejin, Jamilu Sani Tsafe ya fitar, ya bayyana cewa, kwalejin ta riga ta bullo da wani tsari na amfana da fasahar sadarwa ta zamani ba tsabar kudi ba, kuma za ta ci gaba da rungumar fasahar dijital don tabbatar da cewa, kwalejin tana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata da kuma cika ka’idojin duniya.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
