Kasuwanci
Gwamnatin Tarayya Zata Gabatar Da Shirin Wayar Da Kan Jama’a Game Da Muhimmancin Kisan Kasa
Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin wayarda kan jama’a game da Tattalin Arziki wanda zai inganta gaskiya, kishin ƙasa, rikon amana da a duk wani abu na rayuwar ƙasa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ya bayyana haka a wajen bude taron Akanta na shiyyar Arewa na Minna 2025, wanda Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria ICAN ta shirya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Malam Jibrin Baba Ndace, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na Muryar Najeriya, ya bayyana cewa wannan tsarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar nan ba da dadewa ba, an shirya shi ne don kokarin yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar magance ba kawai tsari ba, amma halayya da dabi’un da ke dagula al’amura.
Mohammed Idris ya bayyana cewa, ba da lissafi shi ne ginshikin kowace al’umma mai ci gaba, wanda idan ba shi da amincewar jama’a ke rugujewa, cibiyoyi suna raguwa da ci gaba, a daya bangaren kuma, sake fasalin kasa yana magana ne kan dabi’u, da’a da kuma tsarin tunani na gama-gari wadanda suka daure mu yayin da mutane ke yin hakan tare da samar da taswirar dabi’u da cibiyoyi da ake bukata don budo da dimbin arzikin dan Adam da abin duniya.
Mohammed Idris ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, aikin nasa ya samo asali ne wajen tsara kimar al’umma, samar da amana ga gudanar da mulki da kuma wayar da kan ‘yan kasa wajen cimma manufofin kasa daya.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi gyare-gyaren da ke magana kai tsaye ga wannan batu, kamar shirin bayar da lamuni na dalibai da ke ba wa kowa damar samun ilimi mai zurfi, babbar hanyar Legas zuwa Calabar, babbar hanyar Badagry-Sakoto, gyara hanyar jirgin kasa ta Gabas.
Da yake sanar da bude taron, gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago, ya tabbatar wa mambobin Cibiyar Kula da Akantoci ta Najeriya cewa, daga cikin sama da Naira miliyan dari uku da ta kudiri aniyar aiwatar da ginin ofishinta na shiyya da cibiyar horarwa a Minna, gwamnatin jihar Neja za ta samar da naira miliyan dari da hamsin wanda kashi hamsin cikin dari na kudaden da ake bukata domin gudanar da irin wannan aiki.
A sakon sa na fatan alheri, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi na jihar, Mohammed Bello Auta ya sanar da bayar da gudummawar naira miliyan biyar ga taron.
Shugaban Cibiyar Kula da Akantoci na Najeriya, DR Haruna Yahaya ya bayyana cewa, cibiyar idan aka kammala da fatan a cikin watan Disamba na wannan shekara za ta sanya wa Gwamnan Jihar Neja suna Umar Bago ICAN Centre.
Daga cikin hazikan malaman da suka gabatar da kasidu a wajen bude taron na kwanaki uku na kungiyar ICAN, akwai tsohon mataimakin shugaban jami’ar jihar Kaduna, Farfesa Tanko Mohammed yayin da wakilin Corp Marshal kuma shugaban hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Shehu Mohammed ya gabatar da sakon fatan alheri a wajen taron.
ALIYU LAWAL.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
