Labarai
Gwamnatin Zamfara Ta Jajantawa Iyalan Wadanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana alhininta kan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Juma’a a Nasarawan Kifi, da ke Gundumar Birnin Tudu ta Karamar Hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da ke kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa jirgin ruwan ya ɗauki fasinja ne fiye da ƙima, wanda hakan ya jawo kifewar sa a tsakiyar hanya, inda ya haddasa asarar rayuka da dama.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto da binciko wadanda suka bace, inda ƙungiyoyin gaggawa ke aiki tare da shugabannin al’umma domin tantance adadin mutanen da suka ɓace da kuma bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka tsira.
“A madadin Gwamnatin Jihar Zamfara, muna mika ta’aziyyar mu ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da roƙon Allah ya jikansu da rahama,” In ji sanarwar.
Mahmud Dantawasa ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki don ganin iyalan da abin ya shafa sun samu tallafi da agaji cikin gaggawa.
A cewarsa, Gwamna Dauda Lawal ya umurci jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen gudanar da ayyuka a yankin, domin hana ƙarin hare-haren ’yan bindiga da kuma kare rayukan mazauna ƙauyukan da abin ya shafa.
Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin Zamfara na kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
