Labarai
Shugaban Hukumar KADIRS Ya Ba Da Goyon Baya Ga Rotary
Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Shiga na Jihar Kaduna (KADIRS), Kwamared Jerry Adams, ya ce zai ci gaba da tallafawa kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan lumana da jin kai a jihar.
Adams ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi tawagar Rotary Action Group for Peace, reshen Kaduna, karkashin jagorancin shugabanta, Rotarian Luqman Babatunde, a ofishinsa.
Ya ce, “Babu ci gaba mai ɗorewa da za a iya samu a cikin yanayin tashin hankali, don haka akwai buƙatar ƙarfafa zaman lafiya da ayyukan agaji.”
Ya kuma ƙara da cewa: “Ni ma Rotarian ne. Ina daga cikin waɗanda ke son ganin yadda bil’adama za su samu kulawa, musamman waɗanda suka fi bukata kamar marasa galihu, zawarawa da waɗanda ba su da aiki. A duk inda aka ambaci bil’adama, ya kamata mu bayar da gudummawa, ko da kaɗan ne. Domin ba a haife mu daidai ba, akwai masu ƙarfi, akwai masu rauni, waɗannan mutane kuma suna buƙatar kulawa. Kamar yadda aka ce, duk yatsu ba su daidai ba.”
Adams ya yi kira ga al’umma, musamman masu hannu da shuni, da su tallafa wa Rotary, yana mai cewa: “Gwamnati ba za ta iya yin komai ba ita kaɗai. Shi ya sa muke da kungiyoyi masu zaman kansu kamar Rotary Club, wadda take gudanar da ayyuka masu amfani sosai.”
Tun da farko, Rotarian Babatunde ya bayyana cewa: “Sabuwar shekarar Rotary ta fara ne a watan Yuli tare da shirye-shiryen da za su amfanar da al’ummar Kaduna, musamman marasa galihu.”
A ƙarshe, tawagar ta miƙa wa shugaban KADIRS takardar shaidar Jakadan Zaman Lafiya, wadda aka ba shi a ranar 6 ga Maris.
VOC: Naomi Anzaku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
