Labarai
Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajabta Gudanar Da Gwajin Lafiya Ga Maniyata 2025
Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan maniyatanta na wannan shekarar dolle ne suyi gwajin lafiya cikin wannan makon domin tantance lafiyarsu.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin tantance lafiyar mahajjata kafin gudanar da aikin hajji.
Kuma ya kara da cewa binciken harda tabbatar da mata basu dauke da juna biyu kafin tafiya aikin hajjin.
Yunusa Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki ba domin hana kowa yin Hajji ba ne, sai don tabbatar da cewa an tanadi kula da marasa lafiya musamman ga mahajjatan da ke fama da cututtuka kamar su ciwon sukari da hawan jini.
Ya jaddada cewa sai an yi gwaje-gwajen ne a asibitocin gwamnati da aka amince da su kafin a amince da sakamakon.
“Gwajin lafiya da na ciki wajibi ne. Duk wani maniyaci da ya ƙi samarda tarkardan gwajin na iya rasa gurbin hajjin sa,” in ji sanarwar.
An kuma shawarci mahajjata su karɓi katin lafiyarsu daga hannun jami’an rijista kafin su tafi zuwa asibitocin da aka ware domin gudanar da binciken.
A game da baton abinci, Yunusa Abdullahi yace
za a rika ba mahajjata abinci sau biyu a rana yayin da suke a Saudiyya.
Rel/Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
