Labarai
INEC Tace APC Ce Ta Ci Zaben Kaura Namoda Ta Kudu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana Kamilu Sa’idu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu a jihar Zamfara.
Jami’in kula da zaben Farfesa Lawal Sa’adu na Jami’ar Tarayya da ke Gusau ne ya sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke Kasuwar Daji, hedkwatar mazabar.
A cewarsa, Kamilu Sa’idu ya samu kuri’u 8,182 inda ya doke Muhammad Lawal na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 5,543.
Farfesa Sa’adu ya ayyana Kamilu Sa’idu a matsayin wanda ya cancanta, bayan da ya samu mafi yawan kuri’u.
Sanarwar ta biyo bayan sake zaben da aka gudanar a rumfunan zabe biyar na Sakajiki da Kyambarawa a karamar hukumar Kaura Namoda.
Sake zaben dai ya zo ne bayan kammala zaben farko da aka bayyana bai kammala ba a ranar Asabar din da ta gabata, saboda tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar biyu kasa da adadin katunan zabe na dindindin da aka karba a rumfunan zaben da abin ya shafa.
Sanarwar ta samu halartar kwamishinan zabe na jihar Zamfara, Dakta Mahmud Isah, da kuma wakilan hukumomin tsaro, jam’iyyun siyasa, da kungiyoyin fararen hula.
COV/AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
