Labarai
Gidauniyar Aliko Dangote Za Ta Yi Rabon Abinci Na Miliyoyin Naira A Najeriya
Shahararran Attajirin nan da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi masu azumi su dubu goma a jiharsa ta Kano karkashin gidauniyar Aliko Dangote.
A wata sanarwa da jami’ar gidauniyar a Kano, Samira Sanusi ta fitar, ta ce za kuma a yi rabon buhunan shinkafa har guda miliyan daya da kudinsu ya haura Naira miliyan dubu goma sha uku a fadin jihohi Najeriya 36 da babban birnin tarayya Abuja domin rage radadin halin da yan kasa ke ciki.
Wannan karamci ya biyo bayan rabon biredi dubu ashirin a kullum ga mazauna Kano da kuma dubu goma sha shidda a kullum ga mazauna Legas, da gidauniyar ke yi tun lokacin annobar Korona a shekarar 2020.
Samira Sanusi ta bayyana cewa abincin da za a rika rabawa domin buda baki a wannan watan na Ramadana sun hada da dafadukar shinkafa , da shinkafa da miya , da taliya, da wake tare da kaza da naman Sa, da kuma ruwan sha.

Ta ce ana rarraba abincin ne a masallatan Juma’a, tituna, gidajen yari, da gidajen marayu, da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako mazaunin garin Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karamcin da ya ce ya taimaka masa wajen yin buda baki cikin sauki.
Maikatako, wanda a bayyane yake cikin farin ciki, ya ce cin abinci kyauta zai taimaka matuka ga wadanda ba sa iya samun abin da za su yi buda baki.
Maikatako ya kuma nuna godiya ga gidauniyar Dangote bisa wannan karimcin, inda ya yi addu’ar Allah Ya kara masa arziki Ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.

Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki.
A cewar ta, ta yi farin ciki da samun abinci mai daɗi kyauta a halin da ake ciki yanzu.
“Ba abin da zan ce sai godiya gare ku da Aliko Dangote. Ina rokon Allah ya muku albarka,”
Baya ga rabon biredi da aka yi shekara 4 ana yi kyauta, Samira Sanusi ta ce ana ciyar da mabukata a Kano sama da shekaru 30 da suka shude.
A cewarta, ana hakan ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da kuma wuraren dafa abinci daban-daban.
“Shirin ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano 10,000 a kullum da ya hada da karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare” in ji ta.
USMAN MZ
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
