Labarai
Gwamna Namadi Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Dattijo Alhaji Aminu Dantata
Gwamna Malam Umar Namadi ya bayyana alhininsa bisa rasuwar dan kasuwa kuma fitaccen mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu da safiyar Asabar yana da shekaru 94 a duniya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa a madadin Gwamnatin Jihar Jigawa da al’ummar jihar baki ɗaya, Gwamna Namadi na miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, gwamnati, da jama’ar Jihar Kano, da ma dukkan ‘yan Najeriya baki daya, bisa wannan babban rashi na ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yan ƙasa.
Ta ce Alhaji Aminu Dantata fitaccen ɗan kasuwa ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina ƙasa, bunƙasa tattalin arziki da kuma tallafawa marasa ƙarfi.
“Hikimarsa, sauƙin kai da irin tawali’unsa sun kasance abin koyi ga al’umma da dama Baya ga kasancewa shahararren dan kasuwa, marigayin ya kasance dan kasa nagari mai taimakawa da shawarwari ga dukkan abin da zai kawo cigaban kasarsa.
Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Namadi ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, Ya kuma bai wa iyalansa da duk masu alumma haƙurin jure wannan babban rashi.
Jihar Jigawa ta bi sahun sauran jihohin ƙasar nan wajen jimami da alhini rasuwar gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimar jama’a.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
