Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince Da Dokokin Ilimin Noma da Gyaran Kotunan Gargajiya
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci, wadanda suka hada da kafa sabuwar cibiyar karatu ta gaba da sakandare, da kuma yana gyara dokar kotunan gargajiya na jihar.
Dokar farko ta tanadi kafa Kwalejin Fasahar Noma, da ke Samaru Kataf, bisa dokar kafa Kwalejin Fasahar Noma ta shekarar 2024.

Yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin, Barrista Mahmoud Lawal Isma’ila, dan majalisa mai wakiltar Birnin Zariya kuma Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisa, ya bayyana cewa wannan doka tana da nufin bunkasa koyarwa da bada horo, tare da gudanar da bincike a fannin fasahar noma.
A cewar Barrista Isma’ila, wannan kwaleji za ta kasance cibiyar kwarewa ta musamman a fannin ilimin noma, inda za a koyar da dalibai ilimin aiki da kuma na kimiyya a fannoni daban-daban na fasahar noma domin kara wadatar abinci da ci gaban yankunan karkara a jihar.
A wani ci gaban da ya shafi gargajiya, majalisar ta kuma amince da wani kudiri na gyara Dokar Kotunan gargajiya mai Lamba 9 ta shekarar 2021. Wannan gyara yana da nufin inganta yadda ake gudanar da shari’a a matakin kotunan gargajiya.

Yayin da yake gabatar da rahoton kudirin, Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Zonkwa, Barrista Emmanuel Bako Kantiok, ya bayyana cewa gyaran yana da nufin saukaka gudanar da shari’a tare da tabbatar da saurin yanke hukunci a cikin tsarin shari’ar gargajiya.
“Zai kawo sauyi mai kyau ga Jihar Kaduna saboda zai inganta yadda ake gudanar da shari’a”, in ji shi.
An amince da dukkan dokokin ne bayan tattaunawa da shawarwari daga kwamitoci da masu ruwa da tsaki, wanda hakan ke nuna jajircewar majalisar wajen inganta tsarin shari’a da ilimi a jihar.
SHAMSUDDEEN MANNIR ATIKU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
