Labarai
Milk Value Chain Foundation Da CORET Sun Horasda Mata Harkar Kiwo Da Sarrafa Madara A Kaduna
Gidauniyar Inganta Madara (Milk Value Chain Foundation) tare da haɗin gwiwar Kungiyar Hadin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Africa, wato CORET, sun shirya taron karawa juna sani domin inganta harkar kiwo da samar da isasshen madara a Najeriya, tare da bai wa matasa da mata damar dogaro da kai.
Taron wanda ya gudana a garin Kaduna, ya mayar da hankali kan horar da mahalarta kan sabbin hanyoyin kiwon dabbobi, dabarun samar da ciyarwa, da kuma yadda za su inganta sarrafa madara domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Shirin ya samu goyon bayan ƙungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, da kuma tallafin kuɗi daga gwamnatin Swiss Cooperation.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Gudanarwan CORET, Dr. Abdu Umar Hardo, ya bayyana cewa wannan shiri yana da nufin sauya tsarin kiwon gargajiya zuwa na zamani, tare da samar da damammakin tattalin arziki ga matasa da mata musamman a cikin al’ummomin makiyaya.
Dr. Ardo ya ce aiwatar da wannan shiri da gaske zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da matsalar rashin aikin yi, ba kawai a Jihar Kaduna ba har ma da Najeriya baki ɗaya.
Haka zalika, wakilar gidauniyar Milk Value Chain Foundation, Dr. Bilkisu Yusuf, ta yaba da hadin gwiwar, tare da jaddada muhimmancin amfani da ilimin da mahalarta suka samu domin amfanar al’ummarsu.
A kasidarsa mai taken “Inganta Halittar Dabbobi Don Kara Yawan Madara a Najeriya”, Dr. Sabo Mohammed Abubakar ya bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta zuba jari a fannin kiwo da samar da ciyawa mai inganci domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Wani jami’i daga Hukumar Bada Ilimin Makiyaya ta Kasa, Alhaji Abubakar Lawal Boro, ya bayyana taron a matsayin muhimmin ci gaba wanda zai zama madogara ga makiyaya, tare da fatan shirin zai ci gaba da gudana don tallafa musu da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
Shugaban al’umma na Ladugga, Madakin Ladugga, Alhaji Salihu Yunusa, ya bayyana jin daɗinsa da yadda mambobinsa suka amfana da horon, musamman wajen fahimtar yadda za su inganta hanyoyin tara da sayar da madara.
Daga cikin masu gabatar da kasidu akwai Malam Attahiru Alhassan Jaoji daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, wanda ya gabatar da makala kan “Manufofi da Tsokaci Kan Shirin Sarrafa Madara a Yammacin Afirka,” da kuma Jonathan Jatau wanda ya yi bayani kan dabarun bunkasa yawan madara ta hanyar inganta halittar dabbobi.
Mahalarta taron sun fito ne daga yankunan Damau, Ladugga da Luma Kwasam, dukkansu daga cikin Jihar Kaduna.
Cov: Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
