Labarai
Sarakuna Suna Bada Gudunmuwa Wajen Samarda Lafiya Da Hadin Kan Kasa– Kungiyar Sarakunan Afirka
Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa.
Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar karramawa.
A jawabinsa na karɓar nadin, Alhaji Aliyu Dauda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta amince da gudunmuwar da Sarakuna ke badawa ta sanya su a cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Ya ce hakan zai ba da damar gudanar da aikinsu cikin ‘yanci ba tare da katsalandan ba.
Bikin ya samu halartar manyan baki, shugabannin al’umma da masoya daga sassa daban-daban na kasar, lamarin da ya zame wata babbar alama ta muhimmancin shugabancin gargajiya a Najeriya.
Rel: Adamu Yusuf
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
