Kasuwanci
Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.
A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da tsaron lafiyar jama’a.
Don haka rundunar ta bukaci mazauna kauyen Tsohon Kafi da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe a yayin atisayen.
Abdullahi ya ce, za a sanya ido sosai a kan dukkan ayyukan da kuma gudanar da su a cikin yanayi mai aminci da kulawa.
Rundunar ta kuma yaba da ci gaba da goyon baya da hadin kan al’umma wajen tallafawa kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
KARSHE/USMAN MZ
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
