Fasaha
Abdulsalami ya shawarci Kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso su koma ECOWAS

Tsohon shugaban Kasa, kuma ɗaya daga cikin masu shiga tsakani kan rikicin ƙungiyar ECOWAS da jumhuriyar Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga ƙasashen yanki uku da su koma cikin ƙungiyar.
Wannan ne karon farko da mai shiga tsakanin ya furta cewa, ficewar Ƙasashen Burkina-Faso da Mali da kuma jumhuriya Nijar daga ECOWAS mayar da hannun agogo baya ne.
A cewarsa matakin ƙasashen zai iya kawo naƙasu ga tattalin arzikin yankin.
Janar Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga ƙasashen uku da su dawo cikin garke a yi tafiya da su, domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai23 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
